- (0 Likes)

Hukumar Zabe ta Qasar ta ce hadakar jam’iyyun siyasa na Mista Mahathir sun lashe kujera 115, wadanda suka zarce kujera 112 da suke buqata domin kafa gwamnati.
Mista Mahathir mai shekara 92 ya kada tsohuwar jam’iyyarsa ta Barisan Nasional wadda ta shafe fiye da shekara 60 tana mulkin qasar.
Ya dade da yin ritaya daga siyasa, amma saboda zaben ya dawo domin karawa da tsohon yaronsa a siyasa, Mista Najib Razak.
“Ba mun zo ramuwa ba ne, so muke mu dawo da bin doka da oda,” inji Mista Mahathir bayan samun nasara a zaben.
An shirya za a yi bikin rantsar da shi a jiya Alhamis, wanda zai mayar da shi Shugaban Qasa mafi yawan shekaru a duniya.
Saboda wannan nasarar, an bayyana jiya Alhamis da yau Juma’a a matsayin ranakun hutu a fadin qasar.
Wannan yaqin neman zabe dai ya hada Mista Mahathir da tsohon yaronsa na siyasa, wato Firayi Minista mai ci Najib Razak inda suka fafata.
Comments
Post a Comment