Shugaban Kungiyar Izala ta Kasa, Sheikh Bala Lau, ya bayyana
ra’ayin cewa kamata yayi a rika yanke hukuncin kisa kan dillalan muggan
kwayoyi, domin hakan ya kamace su ganin yadda suke hallaka musamman
matasan kasar nan.
Lau yayi wannan kira ne ga gwamnati yayin da ya ke nuna cewa irin
yadda ake safarar muggan kwayoyi cikin kasar nan, abin tashin hankali ne
ainun.
Ya ce muggan kwayoyi su ne a sahun gaba wajen lalata rayuwar matasa da al’umma.
Malamin ya yi wannan kira ne a lokacin da ya ke tattaunawa da PREMIUM
TIMES a Kaduna. Ya na mai cewa nauyi ne da ya rataya kan gwamnati ta
kare al’ummar ta daga shan muggan kwayoyi.
Ya ce Kungiyar Izala tare da Kungiyar Kiristocin Najeriya na kokarin
ganin ana ci gaba da wayar wa mutanen Najeriya kai game da illolin da ke
tattara da amfani da muggan kwayoyi kamar yadda suka yi wa cutar
Kanjamau, kuma aka sami saukin yaduwar ta a kasar nan.
Comments
Post a Comment