Shugabar jami’ar gwamnatin tarayya dake jihar Jigawa Fatima Batul
Mukhtar ta sanar cewa jami’ar ta hada magungunan cutar daji da siga a
sanadiyyar wani nazari da bincike da dalibin jami’ar ya yi.
Fatima ta bayyana haka ne ranar Litini a taron yaye dalibai da suka kammala karatun su a jami’ar.
Fatima ta ce babbar asibitin koyarwa dake Kano ya yi gwajin ingancin
magungunan amma za a ci gaba da yin gwaji a kan su akai-akai.
A hira da ya yi da PREMIUM TIMES Salihu Ibrahim dalibin makarantar
wanda ya hada magungunan ya bayyana cewa fama da akeyi da cutukan ne ya
kara masa karfin guiwar ganin ya yi bincike kan su sannan ya ga ya hada
wadannan magunguna.
” Barin in baka misali, bincike ya nuna cewa mutane miliyan 1.7 a
Najeriya na fama da cutar siga sannan wasu miliyan 7.7 na kan siradi
waso suna dab da kamuwa da cutar.”
” Mutane da dama sun rasa dukiyoyin su sanadiyyar kamuwa da cutar,
ganin cewa magungunan da ake amfanin dasu don samun sauki na da dankaran
tsada.”
Ibrahim ya kara da cewa ganin haka ne ya sa ya dage wajen ya hada maganin wadannan cutuka da za a iya samu a saukake.
Ya ce zai cigaba da yin bincike kan sauran magungunan da yake aiki a kai.
Comments
Post a Comment