INEC ta zargi Gwamna da yin rajista sau biyu
 sanarwar da ta fitar a daren Alhamis, hukumar zaben Najeriyar ta nesanta kanta daga sake rijistar katin zaben da gwamna Bello ya yi ranar 23 uku ga watan Mayu a ofishinsa da ke Lokoja bayan rijistar da ya yi a shekarar 2011 a birnin Abuja.
Sanarwar ta ce hukumar tana da cibiyar rijista daya tilo ne a ko wacce karamar hukumar kasar domin aikin cigaba da masu yin zabe rijista, tana mai cewar yi wa gwamann rijista a fadar gwamnatin jihar Kogi da ke lokoja ya saba wa doka.



Hukumar ta ce kashi na farko a karamin shashi na daya karkashin sashi na 308, na kundin tsarin mulkin kasar ne ya hanata gurfanar da gwamnan a gaban kotu.
Amman duk da haka ta soke rijista na biyun da gwamnan ya yi, kuma za ta dauki matakan ladabtarwa kan jami'inta da ya sake yi wa gwamnan rijista sabanin tsarin hukumar.
Tun ranar 23 ga watan ne wata kungiya mai suna Kogi for Change ta yi barazanar kai gwaman kotu tana mai cewar laifi ne yin rijistan zabe sau biyu.
 
Na nemi jin ta bakin mai magana da sakataran watsa labaran gwamnan Kingsley Fanwo, amman haka ta bata cimma ruwa ba domin waya
Kuma mai taimaka wa gwamnan kan yada labarai ta rediyo da talabijin, Gbenga Olorunpomi, bai amsa tambayar da muka tura masa ta sakon imail ba.
Saida kuma kafafan yada labarai a Najeriya sun ambato Mista Kingsley Banwo yana cewar gwamna ya shiga wani yanayin da ya tilasta masa sake rijistan ne bayan kokarin mayar da rijistarsa ta farko Kogi daga Abuja ya ci tura.
Matsalar yin rijista fiye da daya na daga cikin matsalolin da ke kawo cikas ga samun sashihin zabe a kasar. Wannan na daga cikin dalilan
 suka sa aka fara amfani da na'urar tantance masu zabe a zaben shekarar 2015 a Najeriyar.

Comments