NDDC TA KARKATAR DA NAIRA BILIYAN DARI DA TAMANIN DA UKU NA CIGABAN YANKIN NEJA DALTA IN JI ODITA JANAR NA KASA
Kimanin N183 biliyan ne a ka karkatar da su daga cikin aljihun NDDC ta hanyoyin da ba su dace ba. Wannan korafin ya fito ne daga bakin Odiata Janar na kasa wato Mr. Samuel Ukura. Mr. Ukura ya dage a kan rahoto na musamman da ke tabbatar da wannan ikirari kuma ya ce duk wanda bai yadda da abinda ya fada ba to ya je gaban majalisun tarayya don kare kansa.
Tun da farko Oditan ya tabbar ma da Majalisun Tarayya sakamakon wannan bincike kamar yadda doka ta tanadar amma kuma shuwagabannin NDDC sun musanta wannan zargi.
Daraktan kudi na NDDC ya ce wannan rahoto yayi wuri da yawa kuma yana kunshe da kurakurai hasali ma dai rahoton na son ya nuna cewa shugancin NDDC na yanzu shi ya karkatar da wadannan kudade.
Ofishin Odita ya ya ce ya yi mamakin yaddan NDDC ke musantawa da kuma kunyata rahoton binciken da kwararru su ka yi.
Ofishin ya cigaba da cewa sai da NDDC ta dauki tsawon watanni goma sha shida kafin ta bada damar binciken da ya kamata a dinga lokaci zuwa lokaci (wato periodic checks) daga 9 Desamba 2011 6 ga Mayu 2013. Hakazalika ya dauki tsawon watanni 16 wato 24 na Afrilu 2014 zuwa 12 ga Agusta 2015 kafin a wallafa rahoton karshe na wannan bincike ga Majalisn Tarayya.
Mr. Ukuru ya cigaba da bayani a cikin rahotanni guda uku na musamman da ya mika wa magatakardan Majalisa wato Salisu Maikasuwa kamar haka; Nera Biliyan 183.7 bakwai na a ka gano sun bata a lokacin binciken lokaci zuwa lokaci da a ka yi tsakanin 2008 zuwa 2012.
An biya kimanin Nera biliyan 70.4 a matsayin kudin somin tabi ga 'yan kwangila amma ba su fara aikin da a ka basu kudin su yi ba, kuma Nera biliyan 90.4 sun tafi a matsayin karin kudin bajet ba tare da bin ka'idojin da su ka dace ba.
Haka kuma an biya Nera biliyan goma a matsayin haraji amma ba babu takardu da hukumar haraji ta kasa da za su nuna shaidar an biya. Kuma an biya kimanin Nera Biliyan 5.8 ga 'yan kwangila a ayyukan da kodai ba a yi su ba, ko an yi watsi da su baya ga harajin Nera biliyan 1.2 da ba a cire ba daga kwangilolin da a ke bayarwa
Rahoton ya cigaba da cewa kimanin Nera biliyan 3.1 ne a ka tura zuwa wasu asusun ajiya ba bisa ka'ida ba, sannan kuma kusan Biliyan 1.7 na adavance din ma'aika ba ya cikin lissafi
Sannan kuma babu hujjar da ke nuna miliyan 785 daga cikin Biliyan 1.1 da a ka ware don sayen kujeru ma wasu makarantu da yankin Neja Delta bayan kuma an ce an biya, to Allah Ya kyauta
Comments
Post a Comment